Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon Manchester United ta sallami Jose Mourinho

0
Kungiyar kwallon kafan kasar ingila, Manchester United, ta sallami kocinta, Jose Mourinho, bayan kungiyar kwallon Liverpool ta lallasata a karshen makon da ya gabata a filin Anfield.
Shugabancin kungiyar kwallon kafan ta tabbatar da wannan labari ne a wata jawabi da suka saki. Jawabin yace:
“Manchester United na sanar da cewa kocinta Jose Mourinho, ya bar jam’iyyar daga yau. Wannan kungiya na nuna godiyarta ga Jose bisa ayyukan da yayi a zamansa a Manchester United kuma muna masa fatan alheri a rayuwa.”
“Za’a nada sabon kocinta rikon kwarya zuwa karshe wannan kaka, yayinda za’a gudanar da aikin neman sabon koci na din-din-din.”
Jose Mourinho ya fara samun matsala ne da wasu mambobin kungiyar kwallon kafan musamman a wannan kaka. Da farko Paul Pogba wanda yake fito-na-fito da shi, sannan Antonio Valencia wannan aka tilasta ta bada hakuri don ya nuna yana son a sallami Mourinho.”
Tsohon kocin FC Porto, Chelsea, Inter Milan da Real Madrid ya so tsayawa a Manchester har na tsawon shekaru 15 amma ko shekaru 3 bai karasa ba.Sources:hausa.legit.ng


Ku Danna Comment Domin Rubuta Ra'ayin Ku A Kan Wannan Post Din

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.